Zanga zangar Masar na kara kamari

Dubun Dubatar jama'a na zanga zanga a Masar
Image caption Dubun Dubatar jama'a na zanga zanga a Masar

Dimbin jama'a sun taru a tsakiyar birnin Alkahira, domin sake yin kira ga shugaba Hosni Mubarak na ya sauka daga mulki.

A Dandalin Tahrir, masu zanga zangar na ta wake-wake na nuna kishin kasa, da kuma kada tutoci, yayin da wasu dubbai kuma suka yi wa dandalin tsinke.

Masu aiko da rahotanni suka ce, ba wani tashin hankali na a zo a gani, to amma masu zanga zangar sun yi tsayin daka.

Su ma sojoji sun ja daga, kuma da alamun suna ba masu zanga zangar hadin kai, inda suka ja layi a kofofin dandalin na Tahrir.

An ce sakatare janar na kungiyar kasashen Larabawa, Amr Moussa, shi ma ya shiga zanga zangar.

A yau ba a ji duriyar magoya bayan shugaba Mubarak ba, wadanda suka kara da masu zanga zangar, a ranakun Laraba da Alhamis