Rashin tsaro a Najeriya kalubale ne ga zabe mai zuwa

Yayinda Najeriya ke tunkarar manyan zabuka, wata matsala da yanzu ake fuskanta a kasar ita ce ta tabarbarewar tsaro.

Ana ganin wannan matsala ta rashin ingantaccen tsaro a kasar a matsayin wani babban kalubale ga zabukan dake tafe.

Kimanin watanni biyu suka rage a gudanar da zabukan, amma har yanzu ana ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula da asarar rayuka a wasu sassa na kasar, kamar Jihohin Filato da Borno.

A Jihar Bauchi ma an sami wani tashin hankali kwanan nan a yankin Tafawa Balewa.

To sai dai kuma hukumnomin tsaron Najeriyar na cewa sun himmatu domin tabbatar da tsaro a gabani da kuma a lokacin zabukan.