Zaben Nijar zai kai ga zagaye na biyu

Sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a jamhuriyar Nijar na nuna cewa sai an kai ga zagaye na biyu, wanda za a gudanar ranar sha biyu ga watan Maris.

Sakamakon da hukumar zabe ta fitar ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya, Malam Muhammadou Issoufou ne kan gaba da kashi talatin da shidda cikin dari na kuri'un.

Tsohon praministan Nijar, Seyni Oumarou ne ya zo na biyu da kashi ashirin da uku cikin dari na kuri'un da aka kada.

Akwai dai jam'iyyu shidda da suka hada kawance a baya cewar zasu mara baya ga duk wanda ya samu kaiwa zagaye na biyu na zaben.