Masu zanga zanga sun hana sojoji shiga dandalin Tahrir

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar adawar a kasar Masar wato kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood, ta ce za ta shiga tattaunawa da gwamnati domin neman mafita daga halin da kasar ta shiga.

Kasar ta girgiza sakamakon makonni biyun da aka shafe ana zanga zangar kyamar gwamnati, don haka kungiyar ta ce za ta gwada ta gani ko a wanne mataki ne hukumomin kasar za su iya amincewa da bukatun alummar kasar.

Wani abin alajabi ya faru a dandalin Tahrir dake birnin Alkahira shine, inda daruruwan masu zanga zangar suka hana dakarun soji shiga cikinsu.

Sun kwanta cikin sanyin ruwan sama domin hana dakarun sojin shiga da tankokin yaki, a wani yunkuri da sojojin ke yi na kora masu zanga zangar zuwa wani sashe na dandalin domin budewa jamaa sauran sassan dandalin.

Sai dai duk da wannan alamari, dangantaka tsakanin dakarun soji da masu zanga zangar, ta kasance cikin kyakkyawar alaka, inda babu wani fargabar tashin hankali a tsakaninsu.

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun ce sun yi imanin cewa sojojin ba za su auka masu ba.