Matan Najeriya na fargabar kada a bar su a baya

A Najeriya yayinda babban zabe ke karatowa, mata na ci gaba da nuna fargaba dangane da makomar su a fagen siyasar kasar.

Wasu matan na ganin cewa akwai yiwuwar yawan mata da ke rike da mukaman siyasa a kasar ya kara raguwa a babban zaben da za'a yi a bana.

Don haka ne su ke kira kan a sake lale akan yanda al'amuran ke tafiya, musamman ma ganin karancin adadin matan da aka tsayar a zaben fidda gwani na Jam'iyyu a kasar.

Su na ganin matukar ba a kawar da dabi`ar amfani da kudi a fagen siyasa ba, to da wuya su kai labari.