Jami'ar kungiyar Commonwealth zata tattauna da hukumomin Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Jami'ar kungiyar kasashen commonwealth zata soma tattaunawa da hukumomin kasar kan wasu batutuwa da suka hada da babban zaben dake tafe

A Najeriya, yau ne mataimakiyar babban sakataren kungiyar kasashen Commonwealth, Mmsekgoa Masire-Mwamba zata soma tattaunawa da shugabannin kasar yayin ziyarar da zata soma a kasar.

Ana sa ran Masire-Mwamba, za ta gana da shugabannin siyasa, da na hukumar zabe, da kuma kungoyoyin kare hakin bil'adama, kafin daga bisani ta yiwa manema labarai jawabi.

Babbar jami'ar ta Commonwealth dai tana wannan ziyarar ne a wani mataki da kungiyar kasashen CommonWealth din tace, na tabbatar da an gudanar da ingantaccen zabe ne a kasar ne.

Najeriya dai na ta shirye shiryen gudanar da babban zaben kasar wanda za'a gudanar a watan Afrilu mai zuwa