An kashe mutane kusan hamsin a Kudancin Sudan

Wasu sojojin Kudancin Sudan
Image caption Wasu sojojin Kudancin Sudan

Rahotanni daga Kudancin Sudan na cewa an kashe mutane kimanin hamsin, a sakamakon fadan da aka kwashe kwanaki uku ana tafkawa tsakankanin dakarun sojin kasar.

Fadan ya barke ne a kusa da garin Malakal dake kan iyaka, a jihar Upper Nile shekaranjiya, inda ya watsu zuwa wasu wuraren uku, bayan da wasu sojoji na kudanci suka ki amincewa su mika makamai, a kuma mayar da su arewacin kasar. A karkashin yarjejeniyar sulhun da aka cinma a 2005, rundunar sojan kasar, da kuma tsoffin 'yan tawayen kudancin Sudan sun kafa wasu rukunonin kungiyoyin tsaro na hadin gwiwa a yankunan kan iyaka masu fama da rikici, irin su Malakal.

A gobe ake sa ran sakamakon karshe na zaben rabagardama zai tabbatar da 'yancin kan kudancin Sudan.