'Yan kudancin Sudan zasu san makomarsu yau

Zaben raba gardama akan 'yancin kan kudancin Sudan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana tsammanin bayyana sakamakon karshe da zai tabbatar da 'yan cin kan kudancin Sudan a yau

Yau ne kuma za'a bayyana sakamakon karshe na zaben raba gardamar da zai tabbatar da 'yan cin yankin kudancin Sudan.

Jami'ai dai sun ce, sakamakon zai nuna cewa, kusan kashi casa'in da tara cikin dari sun amince da raba kudancin kasar da arewa.

Sai dai kuma wakilin BBC a birnin Khartum yace, sabuwar kasar ta kudancin Sudan zata fuskanci manyan kalubale da suka hada da na rashin cigaba.

Zaben raba gardamar da aka yi dai wani bangare ne na yarjejeniyar zaman lafiya ta shekara ta 2005, wadda ta kawo karshen yakin basasar fiye da shekaru ashirin a kasar ta Sudan.