An kashe masu zanga-zanga hudu a Tunisia

Wasu motoci da aka kona a Tunisia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu motoci da aka kona a Tunisia

Mutane akalla hudu ne aka yi amannar an kashe a Tunisia bayan da 'yan sanda suka bude wuta a kan masu zanga -zanga a garin Kef na arewa maso gabashin kasar.

An kashe biyu daga cikinsu ne a lokacin zanga- zangar, ragowar biyun kuma suka cika a hanyar zuwa kai su asibiti, sakamakon raunukan da suka samu.

Dimbin jama'a ne suka yi dafifi a gaban ofishin 'yan sanda a yankin, bayan rahotannin dake nuna cewar wani kwamandan 'yan sanda ya mari wata mata cikin masu zanga- zangar, lamarin da ya harzuka masu zanga -zangar suka yi kokarin kutsa kai cikin ginin. An dai rage tsawon dokar hana fitar dare a Tunisiar da sa'o'i biyu, tun bayan zanga- zangar kin jinin gwamnatin da ta kawar da gwamnatin Shugaba Zine el-Abidine Ben Ali.