Gwamnatin Tunisia ta takawa tsohuwar jam'iyyar dake mulki a kasar birki

Zanga zanga a kasar Tunisia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ma'aikatar harkokin cikin gida a Tunisia ta bada sanarwar dakatar da tsohuwar jam'iyyar dake mulkin kasar daga shiga dukkanin harkokin siyasa.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunisia ta dakatar da jam'iyyar da a da ke mulkin kasar daga shiga duk wasu al'amuran siyasar kasar.

Ma'aikatar ta kuma bada umarnin rufe dukkanin ofisoshin jam'iyyar a fadin kasar

Wakilin BBC yace cikin makonni uku tun bayan tunbuke gwamnatin tsohon shugaba Zainul Abidin Ben Ali, masu zanga-zangar na cigaba da neman a kawar da duk masu nasaba da tsohuwar gwamnatin kasar daga sha'anin mulki.

Ma'aikatar cikin gidan dai tace, an dakatar da jam'iyyar ne kafin a kai ga daukar matakin rushe ta.

Sai dai jamiyyar tsohon shugabankasar tace ta ji wannan sanarwa a kafar yada labaran kasar kamar yadda sauran 'yan kasar Tunisia suka ji

Jam'iyyar tace gwamnatin kasar bata aiko mata ba a rubuce, a saboda haka tace zata garzaya kotu