Wata tawagar kungiyar Commonwealth na ziyara a Nijeriya

Shugaban INEC, Profesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban INEC, Profesa Attahiru Jega

Yayin da babban zabe ke karatowa a Najeriya, wani ayarin kungiyar kasashen Commonwealth ya isa kasar, don ganin irin shirin da Najeriyar ke yi na gudanar da zaben.

Tawagar, wadda ke karkashin jagorancin Mataimakiyar sakatare-janar na kungiyar kasashen commonwealth, , za ta gana da hukumomi, da kungiyoyin farar-hula, da sauran wadanda ke da ruwa-da-tsaki wajen gudanar da zaben.

Tawagar dai ta ce kawo yanzu ta gamsu da irin shirye-shiryen da Nijeriyar ke yi na tinkarar babban zaben dake tafe.

Sai dai wasu a Najeriyar na ganin cewa da wuya ta sauya zane a zaben mai zuwa, ganin irin zarge-zargen tafka magudin da aka rika yi a zabubukan da suka gabata.