Darajar kudin Masar ta fadi kasa warwas

Darajar kudin Masar ta fadi kasa warwas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sai dai har yanzu ana ci gaba da zanga-zanga a dandalin Tahrir

Darajar kudin Masar ta fadi kasa warwas, yayin da gwamnati ke kokarin sake zaburar da tattalin arzikin kasar, bayan an kwashe makonni biyu ana zanga zangar adawa da shugaba Mubarak.

Rahotanni sun ce shugaba Mubarak da iyalansa sun tara dukiya mai dimbin yawa, a shekaru talatin din da ya yi yana mulki.

Gidan talabijin na ABC dake Amurka ya buga wani rahoto, wanda ke nuna cewa iyalan Mubarak sun mallaki fiye da dala biliyan 70.

Wakilin BBC ta fuskar kasuwanci, Mark Gregory ya ce ba za a iya tantance ainihin yawan dukiyar da iyalan Mubarak din suka mallaka ba.

Suaran kafafen yada labarai na duniya da dama dai, sun yi ta watsa wannan labari. Sai dai masu sharhi sun yi amannar cewa, an zuzuta alkaluman ne kawai.

Ana ci gaba zanga-zanga

Rahotanni sun ce iyalan na Mubaraka sun mallaki gidaje a manyan biranen duniya, wadanda suka hada da Manhattan, da California, da kuma London.

Baya ga dunbim dukiyar da su ka mallaka a bankunan Switzerland da Burtaniya.

A ranar Lahadi dai bankuna da sauran masana'antu suka koma bakin aiki, bayan shafe makonni biyu ana zanga-zangar adawa da gwamnati.

Har yanzu dai jama'a na ci gaba da zanga-zanga a dandalin Tahrir, domin tilastawa shugaba Mubarak ya sauka daga kan karagar mulki nan take.

Yayin da shugaban yace zai sauka amma sai wa'adin mulkinsa ya kare a watan Satumba mai zuwa.

Karin bayani