An bada sanarwar karin albashi a Masar

Wasu masu zanga-zanga a Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu masu zanga-zanga a Masar

Sabuwar majalisar zartarwar kasar Masar ta bada sanarwar karin albashin ma'aikatan gwamnati da kashi goma sha biyar cikin dari, a zamanta na farko tun bayan fara zanga- zanga makonni biyun da suka wuce a kasar.

Wakiliyar BBC ta ce tun da farko majalisar ta yi sabbin alkawura na gudanar da bincike kan magudin zaben da aka yi da kuma jami'an da ake zargi da cin hanci.

Har illa yau gwamnatin ta amince da ta ware kudade domin biyan diyya ga wadanda aka wawashewa kayyaki ko aka lalata mu su.