Charles Taylor zai bada bahasi a karon karshe a kotu

Tsohon Shugaban Liberia Charles Taylor
Image caption Tsohon Shugaban Liberia Charles Taylor zai bada bahasi a karon karshe a kotun hukunta manyan laifuka dake birnin Hague

Yau ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake birnin Hague zata cigaba da sauraron jawabin karshe a shari'ar da ake yiwa tsohon shugaban kasar Libaria, Charles Taylor.

An dai shafe shekaru uku ana fafata wannan shari'a da za'a kammala ta ranar Juma'a, kuma a yanke hukunci nan gaba cikin wanna shekarar

Wakilin BBC yace yayin wannan shari'ar dai kotun ta saurari bahasi daga shaidu fiye da dari.

Shi dai Charles Taylor yana fuskantar tuhuma ce ta samar da makamai ga 'yan tawaye yayin yakin basasar kasar Saliyo.