'Yan sanda sun tsare dan takarar gwamna na CPC a Nassarawa

A Nigeria rundunar 'yan sanda ta tabbatar da tsare dan takarar mukamin gwamna a karkashin jamiyyar adawa ta CPC a jihar Nasarawa.

Dan takarar gwamnan, Umar Tanko Almakura an tsare shi ne dangane da zargin da ake masa na kulla kai hari a kan tawagar shugaban kasar Goodluck Jonathan wadda ta je yakin neman zabe a jihar.