CPC ta yi watsi da jerin sunayen 'yan takarar da INEC ta fitar

Jam'iyyar CPC a Najeriya
Image caption Uwar Jam'iyyar CPC a Najeriya tace ba zata amince da sunayen wasu 'yan takarar da INEC ta fitar ba, wadanda suka ci karo da wanda ta gabatarwa da hukumar tunda farko

Uwar jam'iyyar CPC ta kasa ta ce hukumar zaben Najeriya ba ta da hurumin fada mata su waye za su yi mata takara a zaben mai zuwa.

Jam'iyyar ta kuma ce, 'yan takarar da ta sani su ne wadanda ta mika sunayensu ga hukumar zaben kasar.

Engr. Buba Galadima shine sakataren jam'iyyar CPC na kasa kana mamba a kwamitin amitattun jam'iyyar, kuma ya shaidawa BBC cewar 'yan takarar da suka mika sunayensu ga hukumar zaben ta INEC su ne za su yi takara dole.

Sakataren jam'iyyar ya kara da cewar babu yadda za'ayi su amince a canza masu 'yan takara.

'Ya'yan jam'iyyar CPCn a wasu jahohin Najeriya irinsu Kano na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da sunayen da hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC ta wallafa inda ta bayyana sunan, Alhaji Muhammad Sani Abacha a matsayin wanda zai yiwa jam'iyyar takarar gwamnan jihar, maimakon Janar Lawal Jafaru Isa wanda tun da farko aka bayyana a matsayin wanda zai yi takarar.

Wannan mataki dai ya sake bude wani sabon shafin kace-nace a cikin jam'iyyar da ta jima tana fama da rigingimu a jihar ta Kano.

Yayinda bangaren Lawal Jafar Isa ke cewa matakin da hukumar zaben ta dauka ya kauce kai'da, su kuwa bangaren Muhammad Sani Abacha cewa suke, sam barka.