Takkadama kan sunayen 'yan takara a Najeriya

Da alamu an yanka ta tashi dangane da jerin sunayen 'yan takara da hukumar zaben Najeriya ta fitar ranar Litinin a jihohi daban-daban na kasar, sakamakon janye jerin sunayen 'yan takara na jihar Enugu da hukumar ta yi.

Hukumar ta ce umarnin kotu ne ya sa ta dau wannan mataki. Hakan dai ya zo wa wasu da abin ya shafa da ba-zata. Labarin janye sunayen 'yan takarar na jihar Enugu, an yi shi ne kwana guda bayan da hukumar zabe ta kafe sunayen a harabar hedikwatarta da ke birnin Enugun.

Kwamishinan zabe na jihar, Barista Josiah Uwazuruonye, ya shaida wa wakilin BBC a Enugu AbduSsalam Ibrahim dalilinsu na yin hakan : "Dalili shi ne, akwai kuskure game da fito sunayen 'yan takaran, saboda wasu kararraki da ke kotu, kuma a wasunsu ma kotu ta sa mana takunkumi, wanda ya hana mu fitar da sunayen 'yan takarar." In ji Josiah.

Ya shafi duka jam'iyyu

Wani abin da ya daure wa jama'a kai dai shi ne, shin ko wannan mataki ya toge ne ga sunayen 'yan takarar wasu jam'iyyu, ko kuwa dukkan rassan jam'iyyun siyasa na jihar Enugu ya shafa? A nan sai kwamishinan zaben ya ce:

"A'a, umarnin da aka ba mu cewa ya yi, mu janye sunayen 'yan takara na jihar Enugu, umarnin da aka bayar kenan." Matakin janye sunayen 'yan takarar dai, ya shafi hatta gwamnan jihar Enugu, Barista Sullivan Chime, wanda aka bayyana a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, a sunayen da hukumar zaben ta ce ta kafe bisa kuskure a jiya.

Saboda haka, Wakilin BBC ya nemi jin ta bakin Barista Chukwudi Achife, wani mataimaki na musamman na gwamnan jihar Enugun, dangane da wannan batu, ya kuma bayyana cewa, abin ya shammace su: "Ai abin ya zo mana da babbar ba-zata, saboda a ganinmu ba wata hujja da za ta sa a dau wannan mataki. Domin kuwa hukumar zabe ba za ta rasa yin la'akari da duk abin da ya kamata ba, kafin ta kafe sunayen 'yan takarar tun da farko. Amma dai hakan bai girgiza mu ba." Ya kuma jaddada cewa, sun yi amanna duk juyin da aka yi a karshe dai gwamnan jihar ne zai kasance dan takarar jam'iyyar PDP.

Da ma dai magoya bayan wani bangare na jam'iyyar PDP a jihar ta Enugu, tuni suka ga baubaucin kafa sunayen wasu daga cikin 'yan takara da hukumar zaben ta yi a jihar.

Sakamakon bin matakin shari'a da wasu 'ya'yan jam'iyyar suka yi, bisa neman warware takaddamar da ta sarke batun shugabancin reshen jam'iyyar PDP na jihar, da kuma zabubbukan fidda gwani da bangarorinta biyu suka gudanar.

Martanin Hukumar zabe

Hukumar zaben Nigeria mai zaman kanta, INEC ta maida martani ga cece-kucen da fitar da jerin sunnayen 'yan takarar da hukumar ta yi ke haifarwa a wasu sassan kasar.

Image caption Shugaban Hukumar zabe, Farfesa Attahiru Jega

Hukumar zaben dai tace sunayen da ta fitar sune na wadanda suka cancanta su yi takara a zaben mai zuwa, kuma duk wanda yake da wani korafi dangane da hakan, to kofar kotu a bude take.

Mataimakin kakakin hukumar zaben Najeriyar Nick Dazang ya shaidawa BBC cewar sai da hukumar ta tura wasu jami'anta domin su sa ido akan yadda aka gudanar da zabubbukan fidda gwanayen kafin ta kaiga wallafa jerin sunayen 'yan takarar da sukai nasara.

Ya kara da cewa dalilin wallafa sunayen tunda farko shine domin a tabbatar da cewar ainihin wadanda suka ci zaben fidda gwanayen da aka gudanar a baya, sune wadanda aka fitar da sunayensu, sa'annan kuma domin a tabbatar da cewar ba'a tsaida 'yan takara azzalumai ba

Jerin sunayen da hukumar zaben ta fitar dai ya janyo zafafen kalamai daga wasu 'yan takara, da jam'iyyun siyasa, inda har ma wasu jam'iyyun suka zargi hukumar zaben da sauya masu 'yan takara, abunda suka ce INEC din ba ta da hurumin yi.