Jamhuriyar Nijer ta kulla yarjejeniya da Rasha

Hakkin mallakar hoto Reuters

Gwamnatin Nijar ta kulla yarjejeniya da wani banki na kasar Rasha mai suna Gazprombank, domin ya gudanar da binciken Uranium a kasar.

Gwamnatin ta Nijar ta bayar da lasisin ne, a wani mataki na kara samun abokan hulda dangane da maganar hako ma'adinai a kasar.

Tuni dai wasu kungiyoyi a Nijar din suka shiga yin kira ga gwamnatin da kuma Gazprombank, na su mutunta kundin tsarin mulkin kasar, ta yadda 'yan Nijar za su ci gajiyar arzikin ma'adinan.