William Hague na Burtaniya na ziyara a Tunisia

Sakataren hulda da kasashen wajen birtaniya William Hague
Image caption Sakataren hulda da kasashen wajen birtaniya William Hague na yin wata ziyara a karon farko zuwa kasashen da jama'a ke bukatar sauyi

Sakataren hulda da kasashen wajen Birtaniya, William Hague ya soma wata ziyara a Tunisia, a farkon ziyararsa zuwa kasashen arewacin Afurka da kuma yankin gabas ta tsakiya inda jama'a suke neman sauyi a siyasance.

Shi dai Mista Hague shi ne babban jami'in gwamnatin wata kasar yammacin duniya da ya kai ziyara zuwa kasar ta Tunisia, tun bayan boren da ya kai ga tumbuke gwamnatin

zai fara ne da inda aka soma zanga zangar wato kasar Tunisia, inda kuma aka kifar da gwamnatin shugaba Bin Ali a watan daya gabata.

Babban sakon da yake dauke dashi ga gwamantocin da zai gana dasu dai shine cewar birtaniya zata basu goyan baya a aikace da kuma na siyasa domin taimaka masu samar da sauyi mai ma'ana ga alummominsu da kuma gina cibiyoyin dmaukradiya a kasashen.

Birtaniya nada ra'ayin cewar rashin zaman lafiya da kuma tashin hankali na yin barazana ga yankin, matukar aka kasa warwarewa matasa abinda ke harzuka su, ta hanyar gudanar da sauyi ingantacce.

Sakataren harkokin wajen birtaniyan zai je kasashe da dama amma banda kasar Masar.