Zanga-zanga a Masar ta soma bazuwa kan tituna

Zanga-zanga gaban majalisar dokoki a Alkahira Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tsugune ba ta kare ba

Dubun dubatar masu zanga zanga dake bukatar ganin cewa shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, ya sauka daga mulki, ba tare da bata lokaci ba, sun sake hallara a tsakiyar birnin Alkahira, inda suka bazu zuwa wasu sassan da basu cikin dandalin Taharir.

Daruruwan masu zanga-zangar sun yi wa gine-ginen gwamnatin kasar kawanya, ciki hada da majaisar dokokin kasar da kuma ma'aikatar da ke karkashin fadar shugaban kasa.

Wakilin BBC ya ce yau ita ce rana ta goma sha shidda da ake gudanar da zanga zanga a birnin Alkahira.

Kuma babu wata alama dake nuna cewa zanga-zangar ta fara yin kasa, duk da gagarumin fitowar da aka yi a ranar Talata din data gabata, wanda shi ne mafi girma zuwa yanzu.