An samu raguwar masu fama da cutar HIV a Zimbabwe

Cutar HIV mai karya garkuwar jiki Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sakamakon wani bincike ya nuna cewar an samu raguwar masu kamuwa da cutar HIV mai karya garkuwar jiki a kasar Zimbabwe

Sakamakon wani bincike da aka wallafa yau ya nuna cewa, cikin shekaru goma, an samu raguwar wadanda ke kamuwa da kwayar cutar HIV mai karya karguwar jiki a kasar Zimbabwe.

Zimbabwe dai a da na daga cikin kasashen da suka fi yawan wadanda ke kamuwa da cutar.

Adadin wadanda ke kamuwa da cutar dai ya ragu ne daga kashi 29 bisa 100, zuwa kashi 16 cikin 100.

Wakiliyar BBC tace wadanda suka yi wannan bincike dai sun danganta raguwar masu kamuwa da HIV a Zimbabwe ga matakan fadarwar da ake yi ta kafofin yada labaru, da kuma wuraren ibada da wuraren aiki, akan yadda za'a kaucewa kamuwa da cutar.