'Zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya babu tabbas'

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption William Hague

Sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague ya ce yunkurin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya zai iya fuskantar matsala sakamakon rashin tabbas a yankin bayan al'amuran da suke faruwa a Masar da kuma Tunisia.

Mista Hague ya ce akwai tsoro na hakika cewar kokarin samar da zaman lafiya a yankin na Gabas ta Tsakiya zai iya rasa karsashinsa sannan ya bukaci samun kwakkwaran shugabanci daga gwamnatin Obama.

Al'amura da dama za su sauya a Gabas ta Tsakiya.

Ga misali, rikicin siyasar da ke faruwa a Masar zai sauya yadda siyasar yankin take.

Don haka ba abin mamaki ba ne da sakataren harkokin wajen na Burtaniya ya bayyana fargaba a kan yadda shirin tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ta cije.

A yanzu dai duniya ta mayar da hankalinta ne ga Masar.

Kuma kasar ta Masar, wacce Mubarak ke jagoranta, ta kasance mai kare muradun Amurka a yankin na Gabas ta Tsakiya.

Amurka dai na dasawa ne kawai da shugabannin kasashen Larabawan da za su kare bukatunta a kowanne lokaci, duk kuwa da fargabar da take nunawa kan shugabannin kasashen da ba su rungumi tsarin mulkin dimokuradiyya ba.

Manufofin Amurkan dai ba su cika dorewa ba, domin kuwa galibi tana kokawa ne kan shugabannin da ba su yi amanna da muradunta ba.

Shi yasa ma ta kafa wata gamayyar kungiyoyi, wacce take tir da yadda Iran ke dada karfi a yankin.

Kasashen da ke cikin wannan gamayya sun hada da Saudiyya, da Masar, da kuma Isra'ila.

Don haka ba abin mamaki ba ne da cikin shugabannin Saudiyya ya duri-ruwa, ganin abin da ke faruwa a Masar.

Ita ma Isra'ila ta damu sosai dangane da makomar yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kulla da Masar din.

Sauran shugabannin kasashen Larabawa ma na cikin fargaba, ganin guguwar sauyin da ke kadawa a yankin.

A yayin da hakan ke faruwa, sakataren harkokin wajen Burtaniyar, William Hague, yana kira ga Amurka ta nuna dattaku don maido da tattaunawar zaman lafiya a yankin.