Jam'iyyar PNDS a Nijar ta sami goyon bayan Lumana

Tutar Nijar
Image caption Ko ina kawance ARN ya kwana ke nan?

A jamhuriyar Nijar jam'iyar MODEN Lumana Afrika ta Malam Hama Amadu ta ce za ta mara baya ga dan takaran jam'iyyar PNDS Tarayya ta Alhaji Mahamadu Isufu a zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

Jam'iyar ta bayyana matsayin nata ne da marecen yau cikin wata sanarwa da ta fitar bayan wani taro da ta kira a Yamai.

Idan har hakan ta tabbata, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PNDS zai iya samun nasara.

Kana jam'iyyun biyu za suna da karamin rinjaye ke nan a majalisar dokoki idan suka yi aiki tare.