Amurka na cigaba da matsawa kasar Masar lamba

Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden
Image caption Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci kasar Masar data soke dukkanin dokokin ta bacin dake kasar, ta kuma daina dukan 'yan jaridu

Amurka na cigaba da matsa lamba ga shugaban Masar, Hosni Mubarak, domin ya sauka daga kan karagar mulki nan bada jimawa ba.

A wata hira ta wayar tarho, mataimakin shugaban Amurkan, Joe Biden ya fadawa takwaransa na Masar, Omar Suleiman cewa, ya kamata a soke dukkan dokokin tabaci a kasar ta Masar nan take, sannan a daina dukan masu zanga-zanga da kuma 'yan jarida.

Wakilin BBC yace mataimakin shugaban Amurkan ya kuma fadawa takwaransa na Masar cewa, ya kamata ma'aikatar cikin gida ta yi kaffa-kaffa

Kana yace a daina muzgunawa da kuma tsare masu zanga-zanga.