'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga- zanga a Algeria

Hakkin mallakar hoto Reuters

Dubban 'yan sandan kwantar da tarzoma sun dakatar da zanga zanga a Algiers babban birnin kasar Algeria.

Daruruwan mutane sun taru a cibiyar birnin domin gudanar da zanga zangar, to amma adadin 'yan sandan da suka kasance a wurin ya sanya zanga zangar ba ta wuce wasu 'yan sa'o'i ba.

Su dai jama'a na neman inganta rayuwar su ne da samun karin 'yancin siyasa.

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun ce 'yan sandan sun yi wa birnin Algiers kawanya, kuma an girke dubban 'yan sanda da nufin hana zanga zangar.

Don haka ne ya sa zanga zangar ba ta yi wani armashi ba, to amma masu shiryawa sunce wannan somin tabi ne.