Sin ta doke Japan a matsayin kasa ta biyu a arziki

Tuni Kasar Sin ta kwacewa Japan matsayinta na kasa ta biyu a girman tattalin arziki a duniya.

Wasu alkaluman da aka fitar a birnin Tokyo na nuni da cewa a shekarar 2010, tattalin arzikin Japan din ya karu ne da kasa da kashi hudu cikin dari, wani adadi da bai kai yanda na Sin yake ba.

Alkaluman, wadanda ke nuni da irin ci gaban tattalin arzikin da kasar ta samu a shekarar, su ne suka tabbatarwa da Japan matsayinta.

Bayan shafe fiye da shekaru arba'in tana kasancewa kasa ta biyu a girman tattalin arziki a duniya, yanzu kam Sin ta sha gabanta.

A tsakanin watannin Oktoba zuwa Disambar bara, tattalin arzikin Japan din ya tsuke, sannan a shekarar 2011 ci gaban tattalin arzikin da ta samu bai kai kashi hudu cikin dari ba.

Idan za'a yi kwatancen irin ratar ci gaban tattalin arzikin da ke tsakanin kasashen biyu a baya za'a iya cewa duk wani mutum guda a Japan ya ninka dan Sin sau goma a arziki.

Yanzu dai sauyin lamarin da aka samu ya baiwa mutane mamaki.

Shi dai ci gaban tattalin arzikin Japan din dai ya dogara ne sosai a kan makwabciyar ta Sin.