Kungiyar Commonwealth ta shirya wa zaben Najeriya

Kungiyar Commonwealth ta shirya wa zaben Najeriya
Image caption Commonwealth ta ce Najeriya na da mahimmanci a nahiyar Afrika da duniya baki daya

Kungiyar kasashen Commonwealth ta ce ta shiryawa zabukan da ake shirin gudanarwa a Najeriya nan da watanni biyu masu zuwa.

Mataimakiyar Sakatare Janar ta kungiyar Mmasekgoa Masire-Mwamba, ta fada ranar Laraba bayan kammala ziyarar kwanaki hudu a kasar.

A lokacin ziyararta ta, Ms Masire-Mwamba da 'yan tawagarta sun tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar zaben, sannan ta tabbatar da goyon bayan kungiyar na ganin an yi zabukan cikin lumana da adalci.

Ta shaida wa taron manema Labarai a Abuja cewa: "Commonwealth na daukar zabe da mahimmanci a dukkan kasashen kungiyar".

"Baya ga haka Najeriya na taka rawa sosai a harkokin kungiyar ta Commonwealth, ciki harda samar da Sakatare Janar na kungiyar, a cewar Ms Masire-Mwamba.

"Najeriya na da mahimmanci a nahiyar Afrika da duniya baki daya, tana taka rawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki".

Don haka yana da mahimmanci sosai ga Commonwealth, Afrika da ma duniya cewa Najeriya na shirya zabuka masu inganci.

Ms Masire-Mwamba ta gana da shugabannin jam'iyyun siyasa da Hukumar zaben kasar da kungiyoyin farar hula da na kasashen duniya.

Ta ce: "Na saurari ta bakunansu kan yadda shirin zaben ke tafiya tare da tattauna matsaloli da kuma nasarori. Gaba daya tattaunawar ta yi armashi".

Masu lura da al'amura sun bayyana cewa idan har masu ruwa da tsaki suka hadu wuri guda to za a iya samun zabuka masu inganci, inda sakamakon zai dace da zabin jama'a.