An tursasa wa bankuna rufewa a kasar Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters

A kasar Masar, an tursasa wa bankuna rufewa na karin kwana guda, sakamakon nuna rashin amincewa da ma'aikata ke yi game da cin hanci da rashawa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da sabuwar gwamnatin mulkin sojin kasar ke kokarin shawo kan alummar kasar da su koma bakin aiki.

Majalisar koli ta soji a Masar dai ta ce ta rushe majalisar dokokin kasar tare kuma da soke kundin tsarin mulki.

Wannan dai na daga cikin manyan bukatun masu zanga- zangar da suka hambarar da shugabancin Hosni Mubarak a ranar Juma'ar da ta gabata.

Soke kundin tsarin mulkin dai ba karamin mataki bane na ci gaba, saboda kundin tsarin mulkin ya hana jamiyyu da dama taka rawa a zabuka.

Majalisar koli ta sojin, wadda yanzu haka ke rike da ikon Masar ta bayyana cewa ita ce za ta ci gaba da jan ragamar mulkin kasar har nan da watanni shida, ko kuma bayan an yi zabe.

Wannan jawabi dai ya dadadawa dubban masu zanga- zangar kin jinin gwamnatin da suka yada zango a dandalin Tahrir tun kimanin makonni uku da suka gabata.

Mutanen dai sun bijirewa umarnin da Majalisar koli ta mulkin sojin kasar ta bayar kan cewa su tattara ya nasu ya nasu su koma gida.

Sai dai duk da haka sojojin sun bayyana cewa ba zasu yi amfani da karfi ba, wajen ganin hakan ta yiwu.

Su kuma mutanen sun bayyana cewa zasu bar dandalin ne amma sai sojojin sun basu tabbacin mika mulki ga tafarkin demokradiyya.