Kasashe na ci gaba da bayyana ra'ayinsu akan Masar

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugabannin kasashen duniya sun ci gaba da mayar da martani ga al'amarin da ya faru a Kasar Masar.

A Tunisia in da mutane suka hambarar da na su Shugaban a watan da ya wuce, an yi ta rawa a kan tituna da kuma matsa odar motoci domin bukin murabus din Shugaba Mubarak.

Haka nan ma an yi ta shagulgula a yankunan Palasdinawa inda mutane suka yi ta rera taken kasar Masar.

Kungiyar Hamas mai iko da zirin Gaza, ta ce wannan somin tabi ne na juyin juya hali a Masar.

Jami'an Isra'ila kuwa sun bayyana fatan cewa mika mulkin ba zai shafi yarjejeniyarsu da Masar ba.

A Lebanon kuma kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Hezbollah ta taya Jama'ar Masar murna a kan wannan babbar nasara.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya ce murabus din shugaba Mubarak na nufin cewa an saurari kiraye -kirayen da jama'ar Masar suka yi.