Yau INEC za ta fara baje kolin katin zabe

A Najeriya, yau ne hukumar zabe mai zaman kanta INEC za ta fara baje kolin jerin sunayen masu kada kuri'a.

Za a yi wannan baje koli ne a cibiyoyi dubu dari da ashirin da aka yi wa jama'a rajista a sassa daban-daban na kasar.

Baje kolin zai kwashi tsawon kwanaki biyar, daga Litinin zuwa ranar Juma'a.

Makasudin wannan baje koli dai shi ne domin bitar sunayen mutanen da hukumar ta yi wa rajista.

Wannan kuma ya kasance wani yunkuri da hukumar INEC din ke yi na samar da ingantaccen kundin sunayen masu kada kuri'a, kafin lokacin zaben da ke tafe.