Masar ta fusata da kalaman Amurka

Shugaban Kasar Masar Mr. Hosni Mubarak
Image caption Ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar tace Amurka na kokarin yi mata shishshigi a harkokinta

Ministan hulda da kasashen wajen kasar Masar, Ahmed Aboul Gheit ya fito fili yayi watsi da abinda ya kira, kokarin Amurka na tilastawa gwamnatin kasar Masar ta yi abinda take so.

A wata hira da yayi da gidan talabijin na Amurka, PBS, ministan yace, yana mamakin yadda Amurka take kiran, nan take gwamnatin kasar Masar ta soke dokar tabacin dake aiki a kasar tsawon shekaru talatin

Yace idan Amurka ta fadawa babbar kasa kamar Masar tayi wani abu nan take, tamkar ana tilasta mana ne mu dau wani mataki nan take.

Kasashen biyu dai sun jima suna kawance

Amma Jami'an diplomaciyya na yammacin duniya dai na ganin cewar a 'yan kwanakin nan Amurkan ta fara juyawa kasar Masar din baya.