Kungiyar Muslim Brotherhood ta goyi bayan sojin Masar

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar adawa a kasar Masar ta 'yan uwa Musulmi wato Muslim Brotherhood, ta bayyana cewa sam ba za ta nemi iko a kasar ba.

Kungiyar ta fitar da wata sanarwa dake nuna goyon bayanta ga sojoji, tare da bayyana cewa sam ba ta da sha'awar tsayawa takarar shugabancin kasar, ko kuma neman kujeru mafi rinjaye a Majalisar dokoki.

Sai dai ta bayyana cewa za ta bada duk wani goyon baya da Majalisar koli ta sojin Masar za ta bukata a yayin mika mulki ga Gwamnatin farar hula.

Wannan dai ya biyo bayan jawabin da Majalisar koli ta sojin kasar Masar ta bayyana kan mika iko ga duk wani wanda 'yan kasar suka zaba.

A jawabin da Majalisar kolin ta fitar, ta bayyana cewa Masar za ta ci gaba da mutumta yarjejeniyoyinta.