Najeriya ta jinjinawa matakin Hosni Mubarak

Najeriya na daya daga cikin manyan kasashe a nahiyar Afrika wacce ke taka rawa a fannin siyasa da kuma zaman lafiya.

A wata sanarwa da gwamnatin Najeriyar ta aikewa da BBC, ministan harkokin kasashen wajen kasar Odien Ajumogobia ya ce Najeriya ta dade tana sa ido akan al'amuran dake faruwa a kasar Masar.

Mista Ajumogobia ya kara da cewa yanzu Najeriya tana maraba da matakin girma da Shugaba Hosni Mubarak ya dauka domin mika mulki kamar yadda jama'ar Masar suka nema.

Wanann jawabin dai ya biyo bayan murabus din da shugaba Mubarak din ya yi, bayan shafe kimanin shekaru talatin yana mulkin kasar Masar.