Jam'iyun siyasa na shirya tunkarar PDP

Yayin da zaben shekarar 2011 ke karatowa a Najeriya, wasu 'yan siyasar kasar na cigaba da tofa albarakacin bakinsu game da yiwuwar hada kan wasu Jam'iyu a kasar domin fuskantar jamiyyar PDP mai mulkin kasar.

Duk dai da akwai Jam'iyu da dama a kasar, batun hadin kai a tsakanin Jam'iyun CPC da ACN shine yafi jan hankalin 'yan kasar.

Sai dai duk da a baya ana ganin wannan hadin kan kamar zai yiwu, Jam'iyun biyu basu cimma wata yarjejeniya ba har lokacin da hukumar zabe ta rufe karbar sunayen 'yan takara.

Yayin dai da 'yan Jam'iyar ACN ke cewa sun yi iya kokarin su wajen ganin an samu hadin kai da Jam'iyar CPC, 'yan Jam'iyar ta CPC na cewa basu ne da laifi ba, wajen kasa cimma wata matsaya tsakaninsu.