An fara samun zaman lafiya a Jos

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A Najeriya duk da rikicen-rikicen dake da nasaba da addini da kabilanci, da kuma siyasa da ake fama da su a Jihar Filato, ga alama dai yanzu haka wasu al'umomin jihar sun fara daukar hanyar zaman lafiya da junansu.

Wannan ya biyo bayan wata yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin wasu al'umomi a yankin Bassa na Jihar.

Ko da yake dai wasu na ganin har yanzu da sauran jan aiki wajen samar da zaman lafiya a Jihar, ganin irin sarkakiya da matsalar Jihar ke da ita.

Jihar dai ta dade tana fama da tashe-tashen hankula wadanda kawo yanzu aka kasa shawo kansu inda ko a kwanan nan sai da aka kashe mutane hudu a karamar hukumar Bassa, kuma yanzu haka mutane a Jihar na ci gaba da barin yankunan da suke ganin na da hadari a gare su.