Dan karamin yaro ya kai hari a Pakistan

Jami'an tsaron kasar Pakistan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani yaro dan makaranta ya kai hari a wata cibiyar daukar soja dake arewa maso yammcin kasar Pakistan

'Yan sandan Pakistan sun ce, wani yaro dan kunar bakin wake, sanye da kayan makaranta ya kai hari a wata cibiyar daukar soja dake arewa maso yammacin kasar.

Harin dai ya hallaka akalla mutane sha hudu, yayin da wasu mutanen da dama suka jikkata.

Dan kunar bakin waken ya kai wannan hari ne dai a garin Mardan, wanda a baya masu tsaurin ra'ayin Islama suka sha kai masa hari

Wakilin BBC yace yanzu dai an kwashe shekaru sojan Pakistan na fafatawa da masu tsaurin ra'ayin Islama dake arewa maso yammacin kasar