EFCC ta gayyaci tsohon Minista Hassan Lawan

efcc
Image caption An dade ana zargin EFCC ta shigar da siyasa a ayyukanta

A Najeriya, Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC, ta gayyaci tsohon ministan ayyuka da gidaje, Dr Hassan Lawan, tare da wasu manyan jami'an ma'aikatar guda hudu.

Hukumar ta gayyace su bisa zargin sama da fadi da kudaden gwamnati ta hanyar bada kwangiloli ba bisa ka'ida ba.

Sai dai magoya bayan tsohon ministan na ganin tashin-tashinar da EFCCn ke masa ba za ta rasa nasaba da siyasa ba, ganin cewa abin ya zo kwanaki kadan bayan da ya bar jam'iyyar PDP mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta CPC.

Sai dai hukumar ta EFCC ta bakin mai magana da yawunta Mr Femi Babbafemi ta yi watsi da wannan zargi.

Mr Femi Babafemi, ya tabbatar wa BBC cewa tsohon ministan ayyuka DR Hassan Lawan ya sake bayyana a ofishin hukumar ta da ke Abuja a safiyar Juma'a, bayan shafe sa'o'i da dama yana amsa tambayiyi a yammacin Alhamis.

Baya ga Dr Lawal, akwai kuma babban Sakatare a ma'aikatar da kuma Daraktan kudi da Daraktan da ke kula da ayyukan manyan hanyoyi da jami'in dake bindiddigin yadda ake bada kwangila.

'Siyasa ce kawai'

Femi Ya ce: "Mun samu bayanai kan almundahana da bada kwangiloli ba bisa ka'ida, wadanda suka haifar da yin sama da fadin kudaden gwamnati da suka tasamma naira miliyan dubu hamasin, inda kuma ake zargin sa da sauran manyan jami'an ma'aikatar da aikata wa".

Sai dai sakataren jam'iyyar CPC na kasa Eng Buba Galadima ya shaida wa BBC ta waya cewa kamen na DR Lawal siyasa ce kawai:

"Saboda babu wanda ya yi korafi a kansa illa dai kawai suna bakin ciki da ganin ya koma jam'iyyar CPC," a cewar Buba Galadima.

Hukumar EFCC dai ta ce ba za ta fadi mataki na gaba da za ta dauka kan tsohon ministan da sauran jami'an da ake zarginsu tare ba, har sai ta kammala bincike.

Wakilin BBC Naziru Mika'il a Abuja, ya ce an dade dai ana zargin manyan jami'an gwamnati a Najeriya da yin sama da fadi da kudaden jama'a dominm azirta kawunansu.

Kuma hukumomin da aka kafa domin yakar wannan dabi'a, ba sa taka rawa kamar yadda mafi yawan 'yan kasar ke fata.