An kashe mutane biyar a jihar Pilato

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya na cewa an kashe mutane biyar, tare da jikkata wasu karin mutane takwas a wani farmaki da wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka kai jiya da dare, a wani wuri da ke kusa da garin Kaduna Vom, a karamar hukumar Jos ta Kudu.

Jihar Filato dai ta dade tana fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini, da kuma siyasa, inda ko a cikin watanni biyu da suka gabata, daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu.

Har ya zuwa yanzu an kasa shawo kan lamarin, yayin da ake tunkarar manyan zabuka a Nijeriyar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Plateau, Abdulrahaman Akano, ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya ce tuni aka kai gawar wadanda aka kashen dakin aje gawarwaki na wani asibiti.