Shugaba Hosni Mubarak na Masar ya yi murabus

Shugaba Hosni Mubarak na Masar ya yi murabus, bayan da masu zanga-zanga suka matsa masa lamba.

Mataimakin shugaban kasa Umar suleoman ne ya bada sanarwar murabis din shugaban.

Dubban 'yan kasar Masar sun fita kan titunan a birnin Alkahira, suna murnar abin da suka dade suna nema.

Masu zanga-zangar sun shafe makwanni uku suna neman shugaban kasar ya sauka.

Muna dauke da karin bayani