An samu asarar rayuka a kudancin Sudan

Sojoji a yankin kudancin Sudan sun ce, yawan mutanen da suka hallaka, a karawar da aka yi tsakanin wata kungiyar tawaye da rundunar sojan kudancin Sudan din, ya haura dari.

A cewar wani kakakin sojojin, yawancin matattun fararen hula ne, wadanda aka rutsa da su a fadan da ya barke a lardin Jonglei.

Rundunar sojan kudancin Sudan din ta zargi madugun 'yan tawaye, Janar George Athor, da keta yarjajeniyar dakatar da bude wutan da aka sawa hannu, kwanaki kamin kuri'ar raba-gardamar da ta baiwa yankin 'yancin kai.

Amma Janar Athor ya ce, sojojin ne suka kai hari akan mayakansa.