An tuhumi Musharraf da kisan Benazir Bhutto

Pervez Musharraf
Image caption Pervez Musharraf

Wata kotun yaki da ta'addanci a Pakistan, dake binciken kisan gillar da aka yi wa fitacciyar jagorar siyasar nan, Benazir Bhutto, ta fitar da waranti na kama tsohon shugaban kasar, Pervez Musharraf.

Masu gabatar da kara sun ce yana sane da shirin Taliban na kai hari a kan Ms Bhutto, amma bai sanar da hakan ga hukumomin da suka dace ba.

An kashe Benazir Bhutto ne cikin watan Disamban 2007, yayinda take barin wani wurin gangamin yakin neman zabe.

Mr Musharraf dai na gudun hijira na kashin kai a London, kuma wani kakakinsa ya ce dalilan siyasa ne suka sa aka bada waranti, don haka tsohon shugaban kasar ba zai yi aiki da ita ba.