Mutanen Yemen na koyi da zanga-zangar Masar

zanga-zangar Yemen Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga a Yemen

Dubban mutane sun hau kan tituna suna zanga zanga a Sanaa babban birnin kasar Yemen, a yunkurin koyi da zanga zangar kasar Masar.

Sun rika ambaton shugaba Ali Abdullah Saleh, suna kira gare shi da ya sauka daga mulki.

Zanga zangar ta kara zafi ne bayan da wasu magoya bayan gwamnati suka farma wani dan karamin gungu na masu zanga zangar a kusa da Jami'ar Sanaa.

Akwai rahotannin dake cewa jami'an tsaro ma sun shiga cikin lamarin.

Shugaba Abdullah Saleh dai yayi alkawarin sauka daga mulki a 2013, amatakin da masu zanga zanga suka ce an dauka da nufin kaucewa aukuwar irin tarzomar da ta barke a Tunisia da kuma Masar.