An kammala zaben majalisar dokoki a Chadi

Sojojin Chadi
Image caption Sojojin Chadi

An rufe rumfunan zabe a kasar Chadi, inda aka gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki, gabanin na shugaban kasa, nan da watanni biyu masu zuwa.

Zaben wanda shi ne na farko a kasar mai arzikin mai, yana da muhimmanci, domin kuwa shine wanda a karon farko jam'iyyun adawa suka amince su shiga, tun bayan da shugaban kasar,Idris Deby, ya sauya kundin tsarin mulki, domin ya sake tsayawa takara, domin yin wa'adin mulki na hudu.

Masu sa ido na tarayar turai sun ce an yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana, duk da cewar wasu rumfunan zaben an yi makarar sa'o'i biyu kafin a bude su.

Rahotanni sun ce jama'a masu yawa ne suka fito yin zaben a N'djamena, babban birnin kasar.