An dakatar da tsarin mulki a Masar

Field Marshal Mohammed Hussein Tantawi, Shugaban majalisar kolin sojan Masar Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Field Marshal Mohammed Hussein Tantawi, Shugaban majalisar kolin sojan Masar

Kwanaki biyu da karbar mulki, hukumomin mulkin sojan Masar sun bada sanarwar jingine tsarin mulkin kasar, tare da rusa majalisar dokokin kasar.

Kafofin yada labaran gwamnati sun ce, hukumomin sojan za su cigaba da mulki har nan da kimanini watanni shidda, ko kuma har ya zuwa lokacin da za a gudanar da zabubuka a kasar.

An kafa wani sabon kwamitin da zai tsara sabon kundin mulkin kasar ta Masar.

A Alkahira, babban birnin kasar, al'amurra na daidaita sannu a hankali.

An bude bankuna da kantuna da jami'o'i. An kuma koma ga cunkoson jama'a da ababen hawa a kan tituna.

A dandalin Tahrir, inda nan ne matattarar masu zanga zangar neman kafa demokradiyya, sojoji da masu zanga zangar da su ka rage sun ja daga.

Dakarun na yin kira ga masu zanga zangar da su bar wurin. Amma su kuma suna nuna damuwa akan kada a ki yin sauye sauyen da suke bukata.

Minista mai kula da kayayakin tarihi a Masar din, Zahi Hawass, ya ce an sace mahimman kayayaki daga shahararren gidan kallo na birnin Alkahira, wanda ke kusa da dandalin Tahrir.