Shugaba Goodluck ya soke yakin zabe bayan turmutsitsin Patakwal

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya soke gangamin yakin neman zabe biyu da aka shirya gudanarwa a sashen arewa maso gabashin kasar, bayan turmutsutsin da ya auku jiya, a lokacin wani gangamin a birnin Patakwal na jihar Rivers.

Mutane akalla 11 ne suka mutu, lokacin da wani dan sanda ya harba bindiga sama, a yunkurin tarwatsa dafifin jama'ar dake rububin ficewa daga inda aka yi gangamin.

Ofishin shugaban kasa ya ce an soke gangamin da aka shirya gudanarwa a jihohin Borno da Yobe ne, domin nuna alhini da kuma girmamawa ga wadanda suka mutu.

Hukumar 'yan sandan Najeriyar tana gudanar da bincike akan turmutsitsin da ya faru.

Lamarin ya haddasa korafe-korafe game da kwarewar 'yan sandan wajen tabbatar da tsari a tarurrukan jama'a. Sai dai a cewar 'yan sandan, idan dambu yayi yawa ba ya jin mai.