Soji a Masar sun yi kiran kawo karshen yajin aiki

Yaro rike da tuta a wajen zanga-zanga Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daga zanga=zanga zuwa ga yajin aiki

Majalissar mulkin soji ta wucin gadi a kasar Masar ta yi kira ga dukkanin yan kasar ta Masar da su kawo karshen yajin aikin da suke yi.

Su koma bakin aikin ba don komai ba illa don taimaka ma tattalin arzikin kasa.

Majalissar ta mulkin soji ta ce, yajin aikin da kuma dukkanin wata takaddama da ake fama da ita tsakanin ma'aiakata da masu kamfanoni, babu abin da za ta yi illa cutar da kasar baki daya

Mazu zanga-zangar da suka kawo da Hosni Mubarak daga mulki kuma, suna ci gaba da kwararawa dandalin Tahrir, suna neman soji su cika alkawurran da suka yi tukuna, kafin su kuma su kawo karshen zanga-zanga.