Gwamnonin PDP na fargabar rikicin zabe

A Nijeriya, a daidai lokacin da babban zaben kasar ke kara karatowa, wani taro na gwamnonin jam'iyyar PDP, jiya da yamma a Katsina, ya yi kashedin cewar bambancin kabila da addini na barazana ga hadin kan kasar.

Taron na hadin-gwiwa da ya hada gwamnoni goma sha-ukku daga kudu-maso-kudu da kudu-maso-gabas da kuma arewa-maso-yammacin Nijeriya ya koka akan bambance-bambancen da suka ce ana cusawa a harkar siyasa, wadanda suka ce, sun saba da akidar zamantakewa da 'yan mazan- jiya suka gina kasar a kan ta.

Sai dai wasu na kallon taron a matsayin na neman samun goyon baya ne ga Shugaba Goodluck Jonathan a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Aprilu.