INEC ta samu matsaloli wajen wallafa sunaye

Wasu suna duba sunayen 'yan takara
Image caption INEC na fata komi ya tafi lafiya gobe

Rahotanni daga sassa daban daban na Nigeria sun nuna cewa an samu matsaloli a shirin da hukumar zabe ta shirya farawa a yau, inda zata kafa sunayen masu kada kuru'a domin jamaa su je su tantance sunayensu.

A yayin da a wasu wurare, mutane suka isa rumfunan da aka shirya baje wadannan sunaye ba tare da ganin wani jami'i ba, a wasu wuraren kuwa, babu ma'aikatan zaben ballatana ma mutane su je domin duba sunayen.

Mataimakin kakakin hukumar zabe mai zaman kanta, Mr Nick Dazam, ya bayyana dalilan da ya sa ba a fara shirin ba a wurare damar kamar yadda suka shaida wa jama’a cewa za a yi.

Ya ce hakan ya hada da matsaloli da suka samu.

Shi ya sa suke kokarin tabbatar da cewa komi ya tafi daidai a gobe, lokacin da suke sanya ran za a fitar da wadannan sunaye.