Amurka ta jinjinawa masu zanga zanga a Iran

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Barkewar tarzoma a Iran

Sakatariyar kula da harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta jinjinawa magoya bayan masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin Iran, wadanda su ka yi taho mu gama da 'yan sanda a babban birnin kasar na Tehran.

Ta ce zanga zangar ta nuna jaruntakar al'ummar kasar Iran da kuma munafuncin gwamnatin kasar, wacce a makonni uku da suka gabata, ta yabawa zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin Masar.

Madam Hilary ta ce alummar Iran sun dace su sami 'yancinsu, kwatankwakcin irin wanda suka gani a Masar.

An dai gudanar da zanga zangar ne a sako sako na birnin Tehran da kuma wasu sassan kasar.

Rahotanni sun ce mutum daya ya halaka a artabun da masu zanga zangar suka yi da yansanda masu kwantar da tarzoma.