Pirayim Minista Berlusconi zai gurfana gaban kuliya

Pirayim Minista Silvio Berlusconi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Pirayim Minista Silvio Berlusconi na Italiya

Wata mai shari'a a birnin Milan na kasar Italia ta yanke hukuncin cewar wajibi ne Prime Ministan Kasar Silvio Berlusconi ya fuskanci shari'a bisa tuhumar laifin biyan kudi domin yin lalata da yarinya 'yar shekaru goma sha bakwai.

A karkashin dokokin kasar Italia dai, yarinyar ta yi kankata a ce karuwa ce.

Mai shari'ar, Cristina Di Censo, ta tsayar da ranar shida ga watan Aprilu, domin fara sauraren karar.

Wasu alkalai mata guda ukku ne za su yiwa Mr Berlusconin shari'a.

Duka da shi da yarinyar dai sun musanta cewar akwai wata alaka ta jima'i a tsakaninsu.